logo

HAUSA

Yang Jiechi ya halarci taron harkokin tsaro na BRICS karo na 11

2021-08-25 11:17:32 CRI

Yang Jiechi ya halarci taron harkokin tsaro na BRICS karo na 11_fororder_hoto1

Wakilin ofishin siyasa na kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana, shugaban ofishin kwamitin kula da harkokin jakadanci na kwamitin kolin, Yang Jiechi ya halarci taron manyan wakilai kan harkokin tsaro na kasashen BRICS karo na 11 ta kafar bidiyo da aka yi jiya Talata. A yayin taron, Yang Jiechi ya jaddada cewa, ya kamata kasashen BRICS su bi jagorancin shugabannin kasashen biyar, domin karfafa mu’amalar dake tsakaninsu kan manyan tsare-tsare, da fahimtar juna a tsakaninsu, da kuma inganta ayyukan kare tsaro. A sa’i daya kuma, yana fatan za a gudanar da taron ganawar shugabannin kasashen BRICS karo na 13 kamar yadda ake fata.

Ya kara da cewa, ya kamata kasashen BRICS su hada kansu, domin fuskantar kalubalen tsaro, yayin da suke hadin gwiwa wajen yaki da annobar cutar COVID-19. Kuma, ya kamata su girmama kimiyya da fasaha, da kuma nuna adawa da wadanda suke neman siyasantar da aikin gano asalin kwayar cutar. Har ila yau, ya ce, ya kamata su tsaya tsayin daka wajen kare tsarin kasa da kasa bisa jagorancin MDD da dokokin kasa da kasa, ta yadda za a tabbatar da cewa, kasashe masu tasowa za su iya shiga ana damawa da su cikin harkokin kasa da kasa cikin yanayi na adalci. (Maryam)