logo

HAUSA

Babban jami’in kasar Sin zai halarci taron BRICS kan tsaro

2021-08-24 21:10:35 CRI

Babban jami’in kasar Sin zai halarci taron BRICS kan tsaro_fororder_微信图片_20210824210830

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya shaidawa taron manema labaran da aka saba shiryawa Talatar nan cewa, Yang Jiechi, mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, zai halarci taron manyan wakilan kungiyar kasashen BRICS kan batutuwan tsaro ta kafar bidiyo da zai gudana a yau.

Wang Wenbin ya ce, Yang, wanda har ila shi ne darektan ofishin hukumar kula da harkokin kasashen waje na kwamitin kolin JKS, zai halarci taron ne, bisa gayyatar mashawarcin tsaron kasa na kasar Indiya Ajit Doval.