logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta yabawa kasashen BRICS saboda sanarwar da suka bayar ta inganta tsarin kasancewar sassa daban-daban a duniya

2021-06-02 21:23:49 CRI

Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta yabawa kasashen BRICS saboda sanarwar da suka bayar ta inganta tsarin kasancewar sassa daban-daban a duniya_fororder_5f7f3d21f38746508804abfc5266bf37

A yayin ganawar ministocin harkokin wajen kasashen BRICS da aka yi jiya Talata, an fitar da wata sanarwar hadin-gwiwa dangane da ingantawa gami da yin garambawul ga tsarin cudanyar sassa daban-daban a duniya, sanarwar da a cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ta dace da hakikanin halin da ake ciki yanzu, kuma akwai bukata matuka. Kana, sanarwar ta shaidawa duniya hadin-gwiwar kasashen BRICS mai karfin gaske.

Mista Wang Wenbin ya bayyana a yau Laraba cewa, akwai wasu muhimman batutuwa dake tattare da wannan sanarwa. Na farko, an sake jaddada alkawarin da kasashen BRICS suka yi na kyautata tsarin kasancewar sassa daban-daban a duniya. Na biyu, an nanata cewa bai kamata a rika yin shisshigi a harkokin cikin gidan sauran kasashe ba. Na uku, sanarwar ta jaddada cewa ya dace a aiwatar da hadin-gwiwar kasa da kasa bisa tushen samar da moriya ga al’umma, da ingantawa gami da kawo sauye-sauye ga tsarin cudanyar sassa da dama a duniya, ta yadda kasashe masu tasowa gami da kasashe mafi fama da rashin ci gaba, musamman kasashen Afirka, za su kara kudura aniyar su a harkokin duniya. Na hudu wato na karshe shi ne, ya kamata a inganta daidaita harkokin tattalin arzikin duniya ta hanyar yin shawarwari tsakanin bangarori daban-daban.(Murtala Zhang)