logo

HAUSA

IMF ya fitar da rahotonsa game da yanayin tattalin arzikin duniya

2021-04-06 21:13:37 CRI

A yau ne asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya fitar da rahotonsa game yanayin tattalin arzikin duniya, inda ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin duniya zai bunkasa da kaso 6 cikin 100 a shekarar 2021 da muke ciki, inda ake sa ran tattalin arzikin kasar Sin, zai bunkasa da kaso 8.4 cikin 100 a shekarar 2021, kasashen da suka ci gaba kuma, tattalin arzikinsu zai bunkasa da kaso 5.1, yayin da kasashen da tattalin arzikin ke bunkasa da kasashe masu tasowa, tattalin arzikinsu zai karu da kaso 6.7.

A cewar rahoton, babu tabbas game da hasashen ci gaban tattalin arzikin na duniya, kuma hakan ya dogara ne, ga irin ci gaban da aka samu kan annobar COVID-19 da kuma tasirin manufofin da aka dauka.(Ibrahim)

Tasallah Yuan