logo

HAUSA

Shugabar IMF: A karfafa hadin gwiwar kasa da kasa don dakile cutar COVID-19

2021-02-28 17:01:15 CRI

A kwanan baya an gudanar da taron ministocin kudi da shugaban bankunan tsakiya na kasashen G20, inda shugabar asusun ba da lamuni ta duniya IMF, Kristalina Georgieva, ta jaddada cewa, gaggauta aikin yiwa dimbin jama’a allurar rigakafin cutar COVID-19 a kasashe daban daban, zai samar da mafi yawan goyon baya ga kokarin farfado da tattalin arzikin duniya.

A cewar jami’ar, ya kamata a kara saurin samar da rigakafin, ta hanyar yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a samar da allurar rigakafi ga dukkan wuraren dake da bukata.

Kana Madam Georgieva ta kara da cewa, bisa hasashen da aka yi, galibin kasashe masu tasowa za su gamu da asarar kudin shiga da ya zarce na kasashe masu sukuni, nan da shekarar 2022. Don haka ta yi kira ga kasashe daban daban da su dauki kwararrun matakai, don gaggauta aikin yiwa jama’a allurar rigakafi, da baiwa kamfanoni da magidanta karin tallafi, da samar da goyon baya ga kasashen da tattalin arzikinsu ke da rauni. (Bello Wang)

Bello