logo

HAUSA

IMF ya amince da bada rancen dala miliyan 271 ga kasar Namibia domin yaki da COVID-19

2021-04-02 11:39:31 CRI

Asusun bada lamuni na duniya IMF, ya amince da bayar da rancen dala miliyan 271 ga kasar Namibia, domin cike gibin kudin da take bukata na dakile annobar COVID-19.

Cikin wata sanarwa da aka fitar jiya, kakakin ma’aikatar kudi ta kasar, Tonanteni Shidhudhu, ya ce rancen zai samar da kudin da ake bukata na tinkarar matsalolin lafiya na gaggawa da COVID-19 ta haifar, ciki har da sayen riga kafi da aikin yin riga kafin da ake bukata domin magance mummunan tasirin cutar kan tattalin arziki da zaman takewa.

A cewarsa, annobar COVID-19 da tasirinta, sun haifar da wagegen gibi ga kasafin kudin kasar, a lokaci guda kuma, abun da kasar ke samu daga fitar da kayayyaki da hidimomi na fuskantar matsi.

Ya kara da cewa, baya ga haka, kudin na da muhimmanci wajen shawo kan munanan tasirin da annobar ta haifar ga kasashe da dama, kuma kawo yanzu, kimanin kasashe 85 a duniya sun ci gajiyar tallafin asusun na IMF. (Fa’iza Mustapha)