logo

HAUSA

Ministocin kasashen Afrika sun tattauna da UNECA da IMF dangane da tunkarar tasirin COVID-19 kan tattalin arziki

2021-02-10 11:16:05 CRI

Ministocin kudi na kasashen nahiyar Afrika, sun tattauna da sakatare janar ta hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD Vera Songwe, da Manajan Daraktar Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF Kristalina Georgieva, dangane da gaggauta tunkarar tasirin annobar COVID-19 kan tattalin arziki.

Yayin taron da aka yi ta kafar bidiyo, dukkan ministocin sun yi kira da kara yawan kudaden ajiya na ketare na takardar SDR da za a iya amfani da su a lokutan bukatar musamman, zuwa dalar Amurka biliyan 500 da kara samar da damar shiga kasuwanni da karin rance mai rangwame da tsawaita shirin biyan bashi, bisa la’akari da tsawaitar annobar.

Wata sanarwa da hukumar ECA ta fitar, ta ruwaito ministan kudin Ghana, Ken Ofori-Atta na cewa, sanin kowa ne za a ci gaba da fama da annobar nan da shekaru 2 zuwa 3. Don haka me ya sa za a tsawaita lokacin biyan bashin da ake bin kasashen da watanni 6 maimakon 24?

A cewarsa, abun tsoro ne ga duk wani ministan kudi ya shaida ta’azzarar tasirin COVID-19, idan ba shi da wata dabara ta shawo kansu. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha