logo

HAUSA

IMF ya bukaci a ci gaba da daukar kwararan manufofi tunkar rashin tabbas

2020-11-20 10:34:56 CRI

IMF ya bukaci a ci gaba da daukar kwararan manufofi tunkar rashin tabbas

Shugabar asusun bada lamuni na duniya IMF, Kristalina Georgieva, ta yi kira da a ci gaba da daukar kwararan manufofin shawo kan batutuwan rashin tabbas da ake ci gaba da samu yayin da kasashe ke kara fadawa cikin matsalar annobar numfashi ta COVID-19.

Ta ce yayin da ake farin cikin samun ci gaba a fannin samar da riga kafi, matsalar ita ce, tsanantar annobar da mummunan tasirinta a kan tattalin arziki.

Cikin sabon hasashen tattalin arziki da ya fitar a watan da ya gabata, asusun ya ce, tattalin arzikin duniya zai ragu da kaso 4.4 a bana. Sannan ana sa ran wani bangare nasa ya farfado a badi da kaso 5.2.

Da take kira ga gwamnatoci su yi gaggawar daukar mataki tare, ta bayyana wasu muhimman bangarori 3 da ya kamata a lura da su, wadanda suka hada: kawo karshen matsalar lafiya da karfafa matakan farfadowa da gina tubali mai karfi na samun kyautatuwar tattalin arziki a karni na 21. (Fa’iza Mustapha)

Fa'iza Mustapha