in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dade da yin watsi da ra'ayin rigingimun wayewar kai
2019-05-16 19:49:13 cri

Yau yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, tun tuni masana kan huldar kasa da kasa su ka watsi da ra'ayin rigingimun wayewar kai, amma yanzu an sake bayyana ra'ayin domin nuna fiffikonsu a bangaren wayewar kai, gaskiya sun bai wa al'ummun kasashen duniya mamaki matuka, dole ne a mai da hankali kan tsoron da jama'a za su shiga.

Lu Kang ya kara da cewa, har kullum kasar Sin ta nace ga manufar kara karfafa cudaya tsakanin kasa da kasa a bangaren wayewar kai, ta yadda za a cimma burin samun zaman lafiya da wadata mai dorewa, tare kuma da gina kyakkyawar makomar bil Adama.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China