in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gudanar da tattaunawa kan wayewar kai shi ne tabbacin zaman jituwa tsakanin kasa da kasa
2019-05-13 20:14:07 cri

Yau yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, martaba bambancin wayewar kai tsakanin kasa da kasa, shi ne tushen kiyaye zaman lafiya da zaman jituwa tsakanin kasa da kasa, a don haka gudanar da tattaunawa kan wayewar kai, shi zai tabbatar da zaman jituwa tsakanin kasa da kasa. Kasar Sin ta shirya babban taron tattaunawa kan wayewar kan Asiya ne, domin nuna wa kasashen duniya ci gaban da kasashen Asiya suka samu a fannin wayewar kai tare kuma da kara karfafa cudanyar wayewar kai tsakanin kasa da kasa, ta yadda hakan zai taimaka wa hadin gwiwar sada zumunta dake tsakanin kasashe daban daban.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China