Xi ya ce, Asiya tana daya daga cikin wuraren zama masu dogon tarihi na dan Adam, kuma muhimmin wuri na haifar da wayewar kan dan Adam. A cikin tarihin ci gaban nahiyar mai tsawon shekaru sama da dubu daya, jama'ar Asiya sun samu manyan nasarori a fannin wayewar kai.
An samu wayewar kai iri daban daban a nahiyar, wadanda suka rubuta wata wasikar tarihi ta ci gaban wayewar kan Asiya. Yanzu, shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kawancen tattalin arzikin na Turai da Asiya da dai sauransu, sun habaka hanyar mu'amala da ta koyi da juna a fannin wayewar kai.
Wayewar kan Asiya na samun ci gaba a yayin mu'amala da wayewar kan duniya, a sa'i guda kuma ta wadatar da wayewar kan duniya. (Bilkisu)