Shugaban ya ce, a halin da ake ciki yanzu na dinga inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya, da fasahohin sadarwa, da ma kasancewar nau'o'in al'adu daban daban, 'yan Adam na da kyakkyawar makoma a gabansu. Sai dai ya yi nuni da cewa, ana kara samun rashin tabbas a duniya. A ganinsa, taron ya samar da wani sabon dandali na inganta shawarwari, da musaya, da kuma yin koyi da juna a tsakanin kasashen Asiya da ma sauran kasashen duniya. (Lubabatu)