in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping: Duniya daya, al'adun daban-daban
2019-05-13 14:13:42 cri

Shekaru biyar da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi lokacin da ya kai ziyara ta farko a hedkwatar kungiyar UNESCO ta MDD, a cikin jawabin nasa ya ce, "Na ziyarci wurare daban-daban a duniya, abin da na fi so yayin ziyarar shi ne gani da ido al'adu masu bambanci a nahiyoyi daban-daban." Yanzu kuma, za a kira wani taron tattaunawar al'adun Asiya dake jawo hankalin wakilai 2000 na wakilan gwamnatoci ko kungiyoyin fararen hula na kasashen Asiya 47 da na sauran kasashen duniya.

Mista Xi ya ce, ya kamata mu sa kaimi ga mutunta al'adu daban-daban da raya al'adu mai jituwa, ta yadda za a maida al'adu daban-daban su zama wata gada da ta zurfafa zumuncin al'ummomi daban-daban, da sa kaimi ga bunkasuwar bil Adam, da mahadar da ta kiyaye zaman lafiyar duniya. Sin ne ta yi kiran a kira irin wannan taro, don kara tuntuba tsakanin matasa da kungiyoyin fararen hula da yankuna daban-daban da kafofin yada labarai na kasa da kasa, ta yadda za a kafa wani dandali na hadin kai tsakanin masana na fannoni daban-daban, don jama'ar Asiya suna iya more rayuwarsu ta tunani da kara himma da kwazo ga hadin kai tsakanin yankuna daban-daban. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China