in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shanghai ya karbi bakuncin karin masu yawon bude ido a lokacin hutun ranar ma'aikata
2019-05-03 15:15:31 cri

Birnin Shanghai ya karbi bakuncin karin masu yawon bude ido, a kwanaki hudu na hutun murnar ranar ma'aikata da aka fara gudanarwa tun daga ranar Laraba.

Dubban masu yawon shakatawa daga cikin kasar ta Sin da ma baki 'yan kasashen waje, sun bude idanu a gidajen adana kayan tarihi da lambunan shan iska, da dadaddun yankunan koguna, da kuma wurare masu shuke shuke dake da kayatarwa.

Ya zuwa yammacin ranar Alhamis, tsohon garin Zhujiajiao, ya yi cikar kwari da baki 'yan yawon bude ido, sama da duk wani adadi da garin ya taba samu a baya.

Sauran wuraren da suka samu karin baki 'yan yawon shakatawa sun hada da gidajen adana kayan tarihi na Shanghai, da na adana kayan kimiyya da fasaha dake birnin, wadanda su ma yawan jama'a da suka ziyarce su ya haura kaso 80 bisa dari, na adadin yawan jama'a da suka taba ziyartar su a baya.

Shafin yanar gizo na Lvmama.com, mallakar wani kamfanin shirya tafiye tafiye dake birnin na Shanghai, ya ce wurin shakatawa na Shanghai Disneyland, da gandun dabbobi na Shanghai, na cikin wurare da aka fi ziyarta yayin wannan hutu.

Mahukuntan birnin Shanghai sun tsara wasu harkoki na nishadantarwa da yawansu ya kai 70, domin jin dadin masu ziyara, ciki hadda ziyarar yankunan birnin, da nune nunen kayan al'adu, da ziyarar wurare masu ban sha'awa da wuraren dake wajen birnin.

Kamfanin Ctrip mai shirya tafiye tafiye, ya yi hasashen cewa, yawan zirga zirga da za a gudanar yayin wannan hutu cikin kasar ta Sin za su kai miliyan 160. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China