in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kudin da aka kashe a makon hutu na farkon watan Oktoba a kasar Sin ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 1200
2016-10-08 12:10:38 cri

Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta ba da rahoto kan yawan kudin da aka kashe a makon hutu na farkon watan Oktoba wato tsakanin ranekun 1 zuwa 7 ga wata, rahoton da ya nuna cewa, yawan kudin da aka kashe a fannonin sayen kayayyaki da abinci, ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 1200, adadin da ya karu da kashi 10.7 cikin dari idan an kwatanta da makamancin lokaci na shekarar bara.

Rahoton wanda aka fitar a ranar Jumma'a, ya ce an kashe kudade mafiya yawa ne a fannonin sayen zinariya, da lu'u lu'u, da kayayyakin wutar lantarki, da na sadarwa, da kuma motoci masu amfani da wutar lantarki.

A fannin sayen abinci kuwa, wuraren cin abinci sun samu masu sayayya mafiya yawa, mutane da yawa sun gudanar da bukukuwan aure da na murnar ranar haihuwa, da kuma liyafar iyalai a wuraren cin abinci.

Ban da haka kuma, wannan shekara shekara ce da ta cika shekaru 95 da kafa jam'iyyar JKS, kana shekara ce ta ciki shekaru 80 da cimma nasarar Doguwar Tafiyar Kafa da dakarun sojin kasar Sin suka gudanar karkashen jagorancin JKS, don haka wuraren yawon shakatawa na tarihin JKS, sun samu masu ziyara sosai a wannan mako.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China