in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Huang Kunming ya gana da mahalarta taron tattaunawar fasahohin watsa labaru bisa fasahohin 5G+4K
2019-04-23 09:44:45 cri
A jiya ne Mr. Huang Kunming, mamban hukumar siyasar kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wanda ke kula da aikin farfaganda, ya gana da manyan baki wadanda suka halarci taron tattaunawar kirkire-kirkiren dabarun watsa labaru bisa fasahohin 5G+4K.

Huang Kunming ya yaba da gudummawar da kafofin watsa labaru na kasa da kasa suka bayar ga kokarin yada shawarar "ziri daya da hanya daya". Ya kuma bayyana cewa, kafofin watsa labaru na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ganin an yada shawarar "ziri daya da hanya daya" mai inganci. Ya ce, ya kamata kafofin watsa labaru su yi amfani da sabbin fasahohin sadarwa, ta yadda za su hada aikin jarida da fasahohin zamani wajen watsa labaru, ko halarta, har ma yada ayyukan shawarar "ziri daya da hanya daya".

Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin, wato CMG ne ya shirya wannan taron tattaunawa, inda baki fiye da 150 na gida da na waje suka halarta, kuma sun yi musayar ra'ayoyi bisa babban jigon taron. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China