A yayin taron, Mr. Xu Lin, mataimakin shugaban hukumar yayata ayyukan kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya bayyana cewa, aikin yada labaru ya samu ci gaba ne a nan kasar Sin a kai a kai a yayin da ake aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare. A cikin shekaru 40 da suka gabata, aikin yada labaru ya inganta a fili bisa ka'idar girmama dan Adam sakamakon hakan, aikin ya zama wata muhimmiyar hanyar kara yin mu'amala tsakanin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar da jama'a fararen hula. Sannan ana yada labaru ne bisa ka'idar kara yin mu'amala da ketare domin tabbatar da ganin sauran kasashen duniya sun fahimci kasar Sin. Bugu da kari, masu aikin yada labaru su ma sun samu ci gaba, inda suka zama wata kafa dake watsa wa sauran kasashen duniya kyawawan labaru game da kasar Sin.
A farkon shekarun 80 ne, gwamnatin kasar Sin ta kafa tsarin yada labarunta ga waje a hukumance. (Sanusi Chen)