Kwanan baya, shirin habaka yawan kudin da za a kashe ta fuskar samar da kuma yin amfani da bayanai daga shekarar 2018 zuwa 2020, wanda ma'aikatar masana'antu da sadarwa da kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na Sin suka gabatar cikin hadin kai, ya bayyana cewa, ya zuwa shekarar 2020, yawan kudin da za a kashe ta fuskar samar da kuma yin amfani da bayanai zai kai RMB biliyan 6000, adadin da zai ci gaba da karuwa fiye da kashi 11 cikin dari a ko wace shekara.
Matakin da ya bayyana cewa, harkokin samar da kuma yin amfani da bayanai sun kara karfi ta fuskar saye-saye, wadda ta kuma kara yawan kayayyakin da aka samar dake shafar kudi har RMB biliyan budu 15. (Amina Xu)