in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta bukaci a samar da kiwon lafiya na bai daya a nahiyar Afrika
2019-04-08 10:43:54 cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yi kira ga kasashen Afrika su gaggauta aiwatar da tsarin kiwon lafiya na bai daya, wanda ke da muhimmanci wajen rage karuwar barkewar kwayoyin cuta da cuttutukan da ba a yada su daga wani zuwa wani.

Cikin wata sanarwa da WHO ta fitar a Nairobin Kenya, gabanin ranar lafiya ta duniya, Daraktar hukumar a Afrika, Meti Matshidiso, ta ce fadada samun ingantattun hidimomi kiwon lafiya masu sauki, zai inganta cimma muradun ci gaba masu dorewa a nahiyar mafi girma ta biyu a duniya.

Ta ce kyakkyawan kudurin shugabanci da samar da isasshen kudi da kwararrun ma'aikata da kuma ingantattun magunguna su ne kan gaba wajen cimma tsarin kiwon lafiya na bai daya a Afrika.

Hukumar na karfafawa kasashen Afrika gwiwar farfado da manufofi da dokoki domin sukaka zuba jari kan ababen more rayuwa da ake bukata wajen cimma tsarin.

Taken na ranar lafiya ta bana shi ne, ' samar da kiwon lafiya na bai daya", wanda ke da nufin jadadda muhimmancin ingancin kiwon lafiya cikin sauki a kuma kan lokaci, a matsayin hanyar rage tasirin cututtuka akan rayuwar dan Adam. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China