in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin Kenya zai bunkasa amfani da Wechat da Alipay a Afirka
2019-03-26 09:26:32 cri

Babban darektan reshen bankin Equity, wato Finserve Africa, Jack Ngare ya bayyana aniyar bakin ta ganin wanzuwar tsarin biyan kudi ta manhajar Wechat da Alipay a Afirka.

Jack Ngare ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Nairobin kasar Kenya. Ya ce, tuni fasahar hidimar biyan kudin ta kasar Sin ta fara amfani a kasashen Kenya da Uganda da Tanzaniya da kuma Rwanda. Sun kuma yi nisa wajen tallata tsarin ga 'yan kasuwar jamhuriyar demokiradiyar Congo (DRC) nan da karshen wannan shekara, kafin daga bisani, tsarin ya karade kasuwannin nahiyar Afirka.

Jami'in ya ce, bankinsa zai baiwa 'yan kasuwa dake gabashi da tsakiyar Afirka damar karbar kudaden daga masu amfani da tsarin biyan kudi ta manhajar Wechat da Alipay.

Ya kara da cewa, manufar hidimar ta Fintech, ita ce bunkasa musayar kudaden ketare a Afirka, matakin da zai kara bunkasa cinikayya tsakanin Sin da Afirka, ta yadda cinikayya tsakanin sassan biyu zai kara zama na zamani tare da rage bukatar rike kudade lakadan. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China