in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi imani cewa, jama'ar Aljeriya za su iya lalubo bakin zaren hanyar raya kasa da kansu
2019-03-19 19:47:18 cri

Yau Talata 19 ga wata, Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana wa manema labaru cewa, kasar Sin ta yi imani cewa, jama'ar kasar Aljeriya suna da basira, za su kuma iya lalubo bakin zaren hanyar raya kasarsu bisa halin da kasar take ciki. Kana kasar Sin na fatan za a tafiyar da harkokin siyasa a kasar ta Aljeriya yadda ya kamata.

A kwanakin baya ne, shugaba Abdelaziz Bouteflika na Aljeriya ya sanar da janyewa daga takarar shugabancin kasar. 'Yan kasar Aljeriya sun sha shirya zanga-zangar nuna kin amincewa na ganin shugaba Abdelaziz Bouteflika ya ci gaba da mulkin kasar. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China