in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A saurari hirar da shugaba Xi Jinping ya yi da wakilan jama'a
2019-03-13 15:35:16 cri

A yayin da shugaba Xi Jinping ya halarci zaman tattaunawa na tawagar wakilan lardin Fujian dake halartar taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya jaddada cewa, ya kamata a samar da yanayi mai kyau ga yin kirkire-kirkire da kafa sabbin kamfanoni, da sa kaimi ga bunkasa wannan fanni a dukkan zamantakewar al'ummar kasar, don kara karfin kasar Sin na yin tasiri da takara a sauyin yanayin duniya. Kana shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata a samar da sharadi ga kamfanoni kanana da matsakaita da kuma matasa wajen samun ci gaba.

Ya kara da cewa, kasar Sin tana kokarin neman samun wata sabuwar hanya domin ingiza ci gaban huldar dake tsakanin bangarori biyu na zirin Taiwan, ya kamata bangarorin biyu wato babban yankin kasar Sin da lardin Taiwan na kasar su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya da gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a da samar da makamashi, tare kuma da mayar da lardin Fujian a matsayin wuri mafi dacewa, inda 'yanuwa a Taiwan zasu kafa kamfanoni a kai.

1  2  3  4  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China