Rahotanni na cewa, a kwanakin baya ne, firaministan kasar Portugal Antonio Costa ya zanta da jaridar Financial Times ta kasar Ingila, inda ya jaddada cewa, bai kamata ba kasashen kungiyar tarayyar Turai su wuce gona da iri a fannin binciken tsaro don nuna bambancin ra'ayi ga jarin da kasashen da ba na EU ba suka zuba. Kasar Portugal ta fahimci damuwar da wasu kasashe suka nuna game da hadarin dake tattare da yin hadin-gwiwa da kamfanin Huawei wajen amfani da fasahar sadarwar 5G, amma a ganinta, bai kamata a dakatar da ayyukan zamanintar da harkokin sadarwa a kasashen Turai ba.(Murtala Zhang)