in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi Allah wadai da harin Afghanistan
2016-07-25 11:26:32 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Mista Lu Kang, ya yi tir da harin da aka kaddamar a birnin Kabul, hedkwatar kasar Afghanistan a jiya Lahadi 24 ga wata, ya kuma gabatar da ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a yayin harin.

Mista Lu ya bayyana hakan ne yayin da ya zanta da manema labaru a wannan rana, inda ya nuna alhini ga wadanda harin ya rutsa da su, da kuma jaje ga wadanda suka ji rauni. Ya ce, Sin za ta ci gaba da goyon bayan kokarin da gwamnatin kasar Afghanistan take yi na yaki da ta'addanci.

Da yammacin ranar Asabar 23 ga watan nan ne aka kai wasu tagwayen hare hare na kunar bakin wake, kan masu zanga-zanga a birnin na Kabul, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 80, yayin da kuma wasu 230 suka jikkata. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China