in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#2019Taruka2# Kasar Sin za ta yi matukar kokarin sassauta matsalar samun rancen kudi da ake fuskanta
2019-03-05 10:24:27 cri

Gwamnatin kasar Sin ta bayyana cewa, a bana, za ta yi namijin kokari wajen sassauta matsalolin samun rancen da kamfanoni suke fuskanta, har ma suke biyan karin kudin ruwa ga rancen da suka samu. Saboda haka ne, za ta kara karfin rage yawan kudin da wasu matsakaita da kananan bankuna suke ajiyewa a babban bankin kasar, ta yadda za a samar da karin rancen kudi ga kamfanoni masu zaman kansu, ciki har da wasu matsakaita da kanana. Bugu da kari, za ta sa kaimi ga manyan bankunan kasuwanci da su samar da rance na dogon zango ga masana'antun dake samar da kayayyaki. Kana yawan rancen da manyan bankunan kasuwanci mallakar gwamnati za su samarwa kananan kamfanoni da masana'antu ya karu fiye da kaso 30%.

Gwamnatin kasar Sin ta kuma alkawarta cewa, za ta daidaita kudin hidima da wasu bankuna da dilallai suke karba bisa doka, ta yadda za a iya sassauta mawuyacin halin da matsakaita da kanana kamfanoni suke ciki a lokacin da suke hada-hadar kudi. Sakamakon haka, za a tabbatar da raguwar kudin da za a kashe a lokacin da ake hada-hadar kudi. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China