in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar kudin Amurka ta fitar da sabon matakin sanya takunkumi kan Iran
2019-02-14 09:48:04 cri
Ma'aikatar kudin kasar Amurka ta sanar da cewa, za ta kaddamar da matakin kakkaba takunkumi kan kungiyoyi biyu da wasu mutane 9 na Iran, bisa zarginsu da nuna goyon baya ga ayyukan lalata Amurkawa ta yanar gizo da kuma neman bayanan kasar.

Bisa sanarwar da ma'aikatar kudin Amurkar ta fitar, za ta hana amfani da dukiyoyin da wadannan kungiyoyi 2 da mutane 9 na Iran suka ajiye a kasar, sannan Amurkawa ba za su yi cinikayya da su ba.

A kuma wannan rana ne, jagoran kolin kasar Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na intanet, inda ya bayyana cewa, ba zai yiwu a kawar da matsalolin da ke kasancewa tsakanin kasashen Iran da Amurka ta hanyar tattaunawa ba. Ya kuma ce, "Ba za a iya samun dabarar kawar da matsalolin dake akwai tsakanin Iran da Amurka ba. Haka kuma, ba za a iya samun kowane irin sakamako ba idan aka yi shawarwari da bangaren Amurka, in ban da asara da Iran za ta yi." Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya nanata cewa, a ganin Iran, kasar Amurka da wasu kasashen Turai masu zambo ne da ba su isa a amince da su ba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China