in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron MDD da ta amince da wata yarjejeniya kan kaura
2018-12-12 10:27:54 cri
An rufe taron kasa da kasa na MDD kan batun kaura a duniya jiya Talata a birnin Marrakech na Morocco.

Yayin taron na yini biyu, kasashe 150 sun amince da yarjejniyar kasa da kasa da ta shafi zirga-zirgar masu kaura cikin aminci.

Da take jawabi yayin taron manema labarai na rufe taron, wakiliyar MDD na musammam kan harkar kaura Louise Arbour, ta bayyana taron a matsayin muhimmi kan batun kaura da huldar kasa da kasa a tarihi.

Ta kara da yin kira da a magance bayanai marasa sahihanci dake kewaye da batun kaura da yarjejeniyar kasa da kasa, tana mai cewa yarjejeniyar da ba ta da karfin doka, ba ta wajabtawa kasashen yin wani abu ba, haka kuma ba ta yi katsalandan cikin 'yancin wata kasa ba.

Daga bangarensa, ministan harkokin wajen Morocco, Nasser Bourita, ya ce amincewa yarjejeniyar mataki ne na farko, inda ya bukaci masu ruwa da tsaki da su ci gaba da kasancewa kamar yadda suka yi yayin taron, yana mai jadadda muhimmancin huldar kasa da kasa wajen magance batun kaura da sauran batutuwan dake jan hankalin duniya.

A cewar MDD, a yanzu haka, akwai mutane miliyan 258 da suka yi kaura a duniya, adadin da ya karu daga miliyan 173 na shekarar 2000.

Kididdigar MDD ta nuna cewa, tun daga shekarar 2000, sama da masu kaura 60,000 ne suka mutu akan hanya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China