MDD ta ce ana sa ran taron zai amince da yarjeniyoyin Gwamnatocin kasashen duniya kan kaura bisa tsari da sakamakon da aka amince da shi wanda ake wa lakabi da "Global Compact for Safe, Orderly and Regular Migration."
Yarjejeniyar na da nufin raba daukar nauyi tsakanin Gwamnatoci da tabbatar da tsaro da aminci da martaba da kariya da mutunta harkokin masu kaura da 'yan gudun hijra. (Fa'iza Mustapha)