Gasar, wadda za'a gudanar a matakai na daidaiku, da na bibiyu, da kuma matakai na tawaga tawaga, gasar an budeta ne a ranar 5 ga watan Nuwamba a babban filin wasannin kwallon teburi dake Gaborone babban birnin kasar, kuma za'a kammala gasar a ranar 10 ga watan Nuwamba.
Kasashen da zasu shiga gasar wanda Botswana zata karbi bakuncinta sun hada da, Afrika ta kudu Zambia, Zimbabwe, Kenya, Saliyo, Burkina Faso, Tunisia, Madagascar, Comoros, Morocco, Gabon da kuma demokaradiyyar Kongo
An sahhalewa kowace kasa ta gabatar da 'yan wasa maza 3 mata 3.
Sai dai, kasar Botswana mai masaukin baki an lamince mata ta fitar da 'yan wasan maza 5 mata 5.(Ahmad Fagam)