in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Salon wasa mai alaka da keke
2018-08-20 09:00:30 cri

Don biyan bukatun da ake da su a wasanni na nau'ikan wasa daban daban, an kirkiro kekuna iri daban daban.

Da farko dai, akwai keke irin na Cross Country (XC), wanda wani irin keke ne maras nauyi, kuma a dab da tayarsa ta gaba, akwai wata na'urar rage girgiza, yayin da a tayarsa ta baya babu irin wannan na'ura. Da wannan keke za a iya gudu da sauri, haka kuma zai ba mutum sauki idan ana neman a hau gangara da shi. Yawancin kekuna irin na Mountain Bike da muke gani a tituna yanzu sun kasance nau'in Cross Country ne. Mutane na son wannan irin keke domin yana da saukin tukawa, da araha.

Ban da wanna kuma, akwai kekuna na Trail da All Mountains. Wadannan nau'ikan kekuna ne dake kama da juna, domin dukkansu na da na'urorin rage girgiza a dab da tayar gaba da baya. Da wadannan kekuna ne ake iya gudu cikin daji, da kuma filin duwatsu cikin sauki. Sai dai na'urar rage girgizar za ta iya haifar da wuyar tafiya, idan ana son hawan irin wadannan kekuna a cikin hanyoyin mota.

Sa'an nan akwai keke irin na Dual Slalom, wanda aka tsara shi domin gudanar da tseren kekuna tsakanin 'yan wasa biyu. Wannan karamin keke yana iya biyan bukatun 'yan wasa na sauka daga saman wata gangara cikin sauki, tare da tsalle kan kananan tuddai daban daban.

Ban da wannan kuma, akwai sauran nau'ikan kananan kekuna irinsu FR da DJ, wadanda ake iya amfani da su domin yin tsalle, da juya jiki a sama, don nuna fasahohin sarrafa keke, da kuma jan hali na mutum mai hawan keke.

Yayin da ake zabar kekuna, sai a yi la'akari da bukatar da ake da ita. Yawancin mutane da suke amfani da keke na Mountain Bike, na zabar irin wannan keke na Cross Country, domin ban da gudu a duwatsu, yana iya biyan bukatunmu na yau da kullum.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China