in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe mutane 11 a harin Pittsburgh na Amurka
2018-10-28 16:36:11 cri

Kimanin mutane 11 aka hallaka, kana wasu mutanen 6 kuma aka jikkata bayan wasu 'yan bindiga sun bude wuta kan mabiyan addinin Yahudanci dake birnin Pittsburgh, a jihar Pennsylvania, ta Amurka a safiyar jiya Asabar.

Yan sanda sun ce, maharin wani mutum namiji ne dauke da makamai, kuma tuni ya mika wuya yana hannun jami'an.

Mai gabatar da shari'a na gundumar yammacin jihar Pennsylvania, Scott Brady ya tabbatar da cewa, wanda ake zargin sunansa shi ne Robert Bowers, mai shekaru 46 da haihuwa daga yankin Pittsburgh.

Kalaman da Bowers ya wallafa a kafafen sadarwa na zamani ya nuna cewa, yana kin jinin mabiyan addinin Yahudanci.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fadawa taron gangamin jama'a a Indianapolis, na jihar Indiana a ranar Asabar cewa, "Ba za'a laminci kin jinin mabiya addinin Yahudanci ba."

Trump ya ce, "Wannan mummunan aiki ne, kashe jama'a cikakken laifi ne, ba za'a amince da hakan ba, kuma, maganar gaskiya, wani abu ne da ba'a taba tunaninsa ba."

A jiya Asabar babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi Allah wadai da kakkausar murya game da harbe harben a Pittsburgh, in ji kakakinsa.

"Harbe harben na Pittsburgh al'amari ne mai ciwo, wanda ke ci gaba da tunawa da nuna kin jinin mabiya addinin Yahudanci. Yahudawa a duk fadin duniya suna ci gaba da fuskantar hare hare ba tare da wani dalili ba kawai saboda asalinsu. Nuna kyama ga mabiya addinin Yahudanci ya ci karo da manufofin demokaradiyya da shirin zaman lafiya, kuma bai kamata ba lamarin ya faru a karni na 21", in ji sanarwar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China