in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nuna rashin jin dadinta saboda ficewa Amurka daga UPU
2018-10-19 13:02:00 cri

Kasar Sin ta nuna rashin jin dadi sakamakon ficewar kasar Amurka daga kungiyar masu aikewa da sakonnin bai daya ta kasa da kasa wato (UPU) a takaice, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ne ya sanar da hakan a jiya Alhamis.

A cewar rahotanni, da ma tun a ranar Laraba ne fadar White House ta sanar da cewa, Amurka za ta fice daga kungiyar ta UPU.

"Ba mu ji dadi ba saboda matakin da Amurka ta dauka na ficewa daga UPU," kakakin ma'aikatar wajen kasar Sin Lu Kang, shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai. Ya nanata cewa, Amurka ta yi gaban kanta wajen ficewa daga kungiyar, amma wannan babu abin da ya shafi kasar Sin, ya kara da cewa, wannan ba shi ne karon farko da Amurkar ke ficewa daga wasu kungiyoyin kasa da kasa ba.

UPU ta taka muhimmiyar rawa wajen sada dukkannin kasashen duniya da kara kusantar da kasashen duniya da juna, da kuma bunkasa harkokin cinikayyar kasa da kasa, in ji Lu.

Lu Kang ya ce, a ko da yaushe kasar Sin a shirye take ta shiga a dama da ita cikin harkokin gamayyar kasa da kasa, da kuma taka muhimmiyar rawa tare da tallafawa cigaban kungiyar UPU.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China