in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar ECA ta lashi takobin taimakawa nahiyar Afrika magance kalubalen zaman takewa da tattalin arziki da muhalli
2018-10-19 10:12:39 cri
Sakatariyar zartaswa ta hukumar kula da tattalin arziki ta MDD Vera Songwe, ta yi kira ga kasashen Afrika su dogara da hukumar a matsayin cibiyar tuntuba na magance wasu daga cikin kalubalen zamantakewa da tattalin arziki da muhalli da suke fuskanta

Vera Songwe, wadda ta ce galibin kasashen Afrika na fuskantar kalubale iri guda, a wani yanayi da ba a taba fuskanta ba a duniya, ta bayyana kudurin hukumarta na cike gibin da ke akwai wajen magance matsalolin da nahiyar ke fuskanta.

Da take yi wa jakadun kasashen Afrika bayani game da ayyukan hukumar, ta ce ta hanyar aiki tare da kasashe mambobinta wajen tuntuba da aiwatar da ingantaccen bincike da samar da sakamako, hukumar za ta samar da mafitar da za ta gaggauta cimma burin da nahiyar ke son cimmawa zuwa shekarar 2063 da kuma maradun duniya da ake son cimmawa ya zuwa 2030.

Samar da hanyoyin samun ci gaba mai dorewa don gaggauta baza komar tattalin arzikin nahiyar Afrika da inganta ayyukan masana'antu da samar da hanyoyin kirkire-kirkire don samun kudin aiwatar da ayyukan more rayuwa, na daga cikin muhimman bangarorin da ta lashin hukumar za ta taimakawa kasashe mambobinta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China