Da yake tsokaci kan hakan, jami'in tsare tsare a cibiyar dake lura da manufofin cinikayyar Afirka, karkashin hukumar ta ECA David Luke, ya ce manufofin cinikayya da tasirin su, na da matukar sarkakiya da fadin gaske, ta yadda bai dace a barwa gwamnatoci su kadai nauyin lura da su ba.
Mr. David Luke ya ce kamata ya yi sassa masu zaman kansu, da jam'iyyun gama kai, su shiga a dama da su wajen sanya ido da wayar da kai. Ya ce managartan tsare tsaren cinikayya na samuwa ne kadai, idan daukkanin masu ruwa da tsaki a fannin tsara manufofi suka yi hadin gwiwa da juna.
Kaza lika a cewar Mr. Luke, hukumar ECA na maraba, da yadda kasashen Afirka ke kara maida hankali ga kyautata tsarin cinikayya, musamman ta yunkuri da suka yi, na samar da yarjejeniyar kafa yankin cinikayya maras shinge na nahiyar ko AfCFTA a takaice. (Saminu Hassan)