Kafin haka, wani babban jami'in kasar Amurka ya ce, kasar Sin na yunkurin jibge karin sojoji a yankin tekun kudancin kasar, gami da haifar da matsala ga wani jirgin ruwan sojan kasar Amurka, dake aiwatar da 'yancinsa na zirga-zirga a yankin tekun.
Game da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Lu Kang, ya ce, wannan batu karya ce zalla, kuma yunkuri ne na shafa wa kasar Sin kashin kaza. (Bello Wang)