in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gasa Tsakanin Ma'aikata Sinawa
2018-10-02 21:26:25 cri
A 'yan shekarun baya-bayan nan wani dalibi dan kasar Brazil ya ziyarci abokinsa a birnin Beijing na kasar Sin, inda ya jira shi a ofishinsa kafin ya tashi daga aiki. Daga bisani suka je cin abinci dare, sai ya kasa hakuri ya fadawa abokinsa Basine cewa, "Ko Sinawa ku fi son yin aiki ba dare ba rana? Mene ne kake yi a ofis har zuwa karfe 6 na yamma?"

Gamon katar, mujallar Economist dake sharhi kan harkokin tattalin arziki ta rubuta wani sharhi, inda aka tambayi wata daliba Basiniya game da ra'ayinta kan mutanen kasar Jamus yayin da take shirin barin kasar don dawowa gida. Inda bata yi wata-wata ba wajen bayyana ra'ayinta cewa, "Jamusawa suna da dan lalaci." Wannan maganar ta girgiza mutane da dama, ganin yadda aka san Jamusawa da himma da iya aiki".

Idan aka zo ga batun himma, galibin Sinawa sun kware bisa manufa. Tun suna yara, galibi iyaye ka kakannin Sinawa kan fadawa yaran su kan su mayar da hankali ga harkokin karatu sannan su lakanci sabbin abubuwa. A kullum a kan fada musu cewa, aiki yana tafiya da himma sannan ba ya bukatar wasa", "aiki tukuru yana haifar da sakamako mai kyau", sannan "yawan gwaji yana sa a kware".

Lu Xun wani masani a fannin adabin Sinawa na zamani, ya taba fadan cewa, "Babu wanda aka haifa da basira. Na yi kokari kan aikin da nake yi, yayin da wasu kuma ke nasu kokarin a fannin shan kofi." A kasar Sin ta wannan zamani, yayin da wasu iyalan Sinawa suka samu wadata, irin wadannan iyaye maza da mata har yanzu sun himmantu wajen taimakawa 'ya'yansu na ganin sun yi karatu, har ma a wasu lokutan su kan sanya su daukar wasu kwasa-kwasan samun horo bayan an tashi daga makaranta domin ya kara taimaka musu a harkokinsu na rayuwa.

Godiya ga manufofin mahukuntan kasar Sin na yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, kasar Sin ta cimma gagarumar nasarori a cikin shekaru arba'in da suka gabata. Wadannan shekaru arba'in sun taimakawa Sinawa kasancewa masu himma, inganta rayuwar iyalansu, da al'umma da ma kasar baki daya. Wannan ya yi kama da wani filin wasa ne wanda ke da kwararrun darektoci da takardar bayanin wasa mai kyau da aka tsara. Sai dai kuma kokarin 'yan wasa masu basira shi ne ya sa wasan ya yi nasara.

Kafafen yada labaran kasashen wajen sun yi ta watsa rahotannin dake cewa kamfanonin kasar Sin dake gudanar da ayyuka a kasashen waje suna da aniyar daukar Sinawa a matsayin ma'aikatansu maimakon ma'aikatan cikin gida na kasashen da suke gudanar da ayyukan. Har yanzu wadannan rahotanni da suke ci gaba da bazuwa, wadanda ke nuna cewa kamfanonin kasar Sin dake samar da guraben ayyuka suna bada fifiko wajen baiwa Sinawa ayyuka sakamakon yadda ma'aikatan Sinawan suke nuna amincewarsu na gudanar da karin ayyuka sama da wanda aka saba gudanarwa. Sinawa dake ayyuka a kasashen ketare za su iya fada maka cewa akwai tabbaci a mafi yawan irin wadannan ayyuka ana kammala su a cikin wa'adin da aka tsara da kuma yin aikin mai inganci.

Michael Moritz, wanda ya yi hadin gwiwa da Sequoia Capital, ya wallafa wani sharhi a jaridar "Financial Times" a watan Janairun shekarar 2018 mai taken, "Silicon Valley ya yi matukar hikima wajen bin tsarin kasar Sin." A cikin bayanan, ya ce, "Nan (a kasar Sin), manyan manajoji suna halartar wuraren aiki ne tun da misalin karfe 8 na safe kuma ba za su tashi ba har zuwa karfe 10 na dare. Mafi yawa daga cikinsu suna yin hakan ne har na tsawon kwanaki 6 a cikin mako guda — kuma akwai misalai masu yawa dake nuna cewa wadannan mutane suna yin hakan har a kwanaki 7 wato tsawon mako guda ke nan. Injiniyoyi suna da dan banbancin halayya 'yar kadan: suna isa wuraren aikin ne karfe 10 na safe kuma ba za su bar wajen ba har zuwa tsakan dare. Baya ga aikin da suka gudanar na tsawon mako guda, a lokutan hutun sabuwar shekara da hutun tunawa da kafuwar sabuwar kasar Sin, mafi yawa daga cikinsu suna amfani ne da wasu 'yan kwanaki kadan na lokacin hutun."

Ban da ma Sinawa dake aikin kamfanonin da masana'antu, da yawa daga cikin Sinawa jami'an gwamnati suna bin irin wannan tsari na sadaukarwa da yin aiki tukuru. A lokacin da nake aiki a kasashen ketare, na taba zama mai aikin fassara na tawagar jami'an gwamnatin kasar Sin. A tsawon makonni biyu, tagawar jami'an Sinawan sun shafe wadannan kwanaki suna ta yin taruruka da cimma yarjejeniyoyi, daga nan sai suka nufi filin jirgi da yammaci domin kama hanyarsu zuwa waje na gaba. Washe gari, lamarin haka yake bai sauya ba, haka aka ci gaba da yi babu kakkautawa. Wannan al'amari dai haka ya ci gaba har zuwa lokacin da wannan tawagar ta isa filin jirgi don komawa kasar Sin. A aikina na farko da na yi tare da tawagar jami'an gwamnatin Sin a nan ne na fahimci cewar wadannan mutane suna da jajurcewa. Wannan bai zo da mamaki ba bisa yadda kasar take kara samun karfin bunkasuwa a cikin wasu 'yan shekaru nan.

Tabbas, za'a iya cewa ba kowane Basine dake aikin gwamnati a hukuma mai zaman kanta ne yake da cikakkiyar sadaukarwa ba. Amma baki daya, mutane za su iya yin alkalanci da kansu yadda gwamnati ke tafiyar da harkokinta. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito a shekarar 2018 a cikin wani rahotonsa mai suna Edelman Trust Barometer, inda ya nuna cewa, imanin da ake da shi game da gwamnatin Sin ya tsallaka ya karu da maki 8 zuwa kashi 84 bisa 100 a tsakanin al'umma. Irin makamancin wannan hasashen ya fidda alkaluma dake nuna cewa, sama da kashi 89 bisa 100 na mutanen suna da matakin ilmi mai zurfi da kuma hanyar samun kudaden shiga mai tsoka.

Irin wannan muhimmiyar sadaukarwa tsakanin al'ummar Sinawa tamkar a jininsu take. Abu ne mai wahala ka ga an kira mutum aiki yana tsaka da halartar wani biki tare da abokai, ko ka ga mutum na aiki sa'o'i 24 domin cimma wata manufa ta aiki, ko ka ga mutum na aiki har karshen mako, da ma lokutan hutu sai tsakanin wannan al'umma.

Abun tambayar shi ne, shin daga ina wannan jajircewa ta samo asali? Wani yanki daga littafin "The Romance of the Condor Heroes", na marubucin nan dan asalin yankin Hong Kong mai suna Louis Cha, ya samar da amsa mafi gamsarwa game da wannan tambaya, cewar "Jarumi na samun daukaka ne daga irin gudummawar da ya baiwa kasarsa, da al'ummarsa."

Ga matsakaicin Basine, ya yi imani cewa, yana aiki ne domin kansa, da iyalinsa, da kuma kasarsa. "Iyali kuwa su ne karamin kashi na ginin ko wace kasa." Godiya ga ci gaba na tsawon shekaru 40, Sin a yanzu haka ta kai matsayi na biyu a duniya a fannin karfin tattalin arziki, wanda ya bunkasa daukacin sassanta na raya masana'antu. Fadadar kasuwarta ta motocin hawa, da sahun gaba da ta shiga a fannin cinikayya ta yanar gizo, kadan ne daga bangarorin da ta samu ci gaba a cikinsu. Dukkanin wadannan ba za su samu ba, idan Sinawa ba su kasance masu kwazon aiki ba.

Sakataren ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya Jeremy Hunt, ya yi wani furuci yayin taron jam'iyyar Conservative na lokacin kakar shekarar 2015, inda ya ce "Mata ta Basiniya ce, kuma idan har muna son zama cikin jerin kasashe masu cimma nasara nan da shekaru 20, ko 30, ko 40 masu zuwa, lallai akwai bukatar mu amsa tambaya mai wahalar gaske, mai kuma muhimmanci, wato mun shirya kasancewa kasa mai niyyar aiki tukuru kamar yadda sauran kasashen Asiya suka shirya yin aiki ba kakkautawa?" Wadannan kalamai nasa, sun tada kura, kasancewarsu masu tattare da kuskure a siyasance idan an dubi kimar kasarsa.

Wannan fa ba yana nufin Sin kasa ce dake cike da mutane dake aikin wahala, tamkar yadda butunbutumin inji ke yi domin ci gaban kamfanoninsu da gwamnati ba. Hasali ma dai gwamnatin kasar na da dokoki da ka'idoji da aka gindaya, wadanda ke baiwa al'umma kariya, da dama ta samun hutu da walwala, ciki hadda ka'idar yawan sa'o'i aiki, da wasu kwanakin hutu da aka amince da su.

Sai dai kuma duk da haka, har ya zuwa lokacin da Sin za ta zamo cikin kasashen da suka ci gaba a hukumance, zai yi wuya al'ummar kasar sun yi watsi da al'adarsu ta kasancewa masu "aiki tukuru ba kasala." Duba da cewa, wadannan dabi'u ne dake da nasaba da al'adunsu, da suka gada tsawon dubban shekaru.

(Marubuci: Xu Qinduo, mai fashin baki ne a harkokin siyasa na CRI; Masu Fassarawa: Ibrahim Yaya, Ahmad Fagam, Saminu Hassan, dukkansu ma'aikatan sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China