in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Maganar cewar Amurka ta samu hasarori kan dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninta da Sin ba ta da tushe
2018-09-25 11:30:47 cri

Wasu masu sharhi na kasar Amurka sun bayyana cewa, ana samun gibin kudaden cinikayyar kayayyaki tsakanin Amurka da Sin, a sakamakon takara mai cike da rashin adalci da kasar Sin ke haifarwa, kuma kasar Amurka ta samu hasarori a sakamakon hakan. Game da wannan, wakilin ma'aikatar kasuwancin Sin mai kula da shawarwari kan ciniki a tsakanin kasa da kasa, kuma mataimakin ministan kasuwancin kasar Fu Ziying ya bayyana a yau Talata a nan birnin Beijing cewa, wadannan zarge zarge ba su da tushe bare makama.

Fu Ziying ya kara da cewa, bambancin yawan cinikin dake tsakanin Sin da Amurka ya shafi yawan cinikin da suka gudanar, kuma ba ya nufin samun riba ko hasara. Sin da Amurka, suna da bambancin matsayi a fannin samar da kayayyaki a duniya, yayin da Amurka take a matsayi na gaba, Sin ta zama a matsayin baya. Sai dai kamfanonin Sin sun samu kudi daga kerawa, amma Amurka na samun kudi masu yawa a fannonin tsara salon kayyayaki, da samar da sassan inji, da kuma aikin sayarwa.

Har ila yau samun rashin daidaito kan cinikin dake tsakanin Sin da Amurka, yana da nasaba da kayyade fiyar da kayyayaki da Amurka ta yiwa Sin. Hukumomin da abin ya shafa na kasar Amurka sun kiyasta cewa, idan aka sassauta kayyade fitar da kayyayakin zamani masu amfani ga jama'a, yawan gibin kudin da Amurka ke samu daga Sin zai ragu da kashi 35 bisa dari.

Fu Ziying ya kuma nuna cewa, Sin tana son yin kokari wajen kara sa kaimi ga yin ciniki tsakanin bangarorin biyu cikin daidaito, kana tana fatan Amurka za ta amsa kiran Sin a wannan fanni. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China