in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta samar da guraben aikin yi miliyan 375 cikin shekaru 40 da suka gabata
2018-09-17 12:32:59 cri
Kasar Sin ta samar da ayyukan yi kusan 375 daga farkon fara aiwatar da manufarta ta bude kofa ga kasashen waje da gyare-gyare a cikin gida a shekarar 1978 ya zuwa 2017.

Rahoton hukumar kiddidiga ta kasar Sin ya ce, jimilar ayyukan da aka samar a birane da yankunan karkara ya kai miliyan 776 ya zuwa karshen bara, wadda ta karu da kaso 93 kan na shekarar 1978. Jimillar ayyukan da aka samar a birane a karshen 2017 ta kai miliyan 425, adadin da ya karu kan na 1978 da kaso 346.

An samu karuwar guraben ayyukan yi ne sanadiyyar ci gaban tattalin arziki da aka samu. Cikin shekaru 40 da suka gabata, alkaluman GDP na kasar Sin na karuwa da kashi 9.5 a kowace shekara.

A cewar rahoton, cikin shekaru 10 da suka gabata, matakin adadin marasa aikin yi dake da rejista ya yi kasa sosai, inda ya kasance kan kasa da kaso 3.1 tsakanin tsakiyar shekarun 1980 da karshen karni na 20, sannan baya nan, ya kasance kan kaso 4 da 4.3, kafin daga bisani ya sauka zuwa kaso 3.9 a bara.

A rabin farko na bana, adadin ayyukan yi da kasar Sin ta samar ya karu, la'akari da ci gaban tattalin arziki da ta samu, duk da takaddamar cinikayya da ake fuskanta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China