Karon farko hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bullo da sakamakon bincike kan yawan mutanen da suka rasa ayyukan yi a biranen kasar
Karon farko hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bullo da sakamakon binciken da aka yi kan adadin mutanen da suka rasa ayyukan yi a birane da garuruwan kasar, inda suka nuna cewa, a rubi'in farko na bana, mutane da yawa sun samu ayyukan yi a duk fadin kasar Sin. Sannan daga watan farko zuwa na uku na bana, yawan mutanen da suka rasa ayyukan yi a birane da garuruwan kasar ya kai kashi 5 bisa dari, da kashi 5 bisa dari da kuma kashi 5.1 bisa dari, wadanda suka ragu da kashi 0.2 bisa dari, da kashi 0.4 bisa dari da kuma kashi 0.1 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara. (Murtala Zhang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku