Sakatare Janar na Majalisar mai ci Antonio Guteress shi ma ya shiga cikin mambobin kwamitin 15 yayin da suka yi shirun.
An yi shirun na minti guda ne a farkon taron manyan jami'an kwamitin da ya gudana karkashin jagorancin Sakataren harkokin wajen Birtaniya Jeremy Hunt, wanda kasarsa ke rike da shugabancin kwamitin a watan Augusta.
Kofi Annan mai shekaru 80, dan asalin kasar Ghana, kuma jami'in diflomasiyya, wanda ya taba samun kyautar karramawa ta MDD ta Nobel kan zaman lafiya, ya mutu ne a ranar Asabar da ta gabata a Switzerland. Marigayin ya rike mukamin Sakatare Janar na MDD tsawon shekaru 10. (Fa'iza Mustapha)