A cikin sakon, shugaba Xi ya kuma mika ta'aziya ga iyalan wadanda harin ya rutsa tare da jajantawa iyalan wadanda suka jikkata. Xi ya ce ta'addanci babban makiyin bil-adam ne, kuma kasar Sin ba ta goyon bayan duk wani nau'i na ta'addanci, kana ta yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai a kasar Pakistan.
Shugaba Xi ya ce, har kullum Sinawa na tare da al'ummar Pakistan, suna kuma goyon bayan matakan da kasar ke dauka na yaki da ayyukan ta'addanci, da tabbatar da zaman lafiya da kare rayukan al'umma. (Ibrahim)