Da yake gabatar da jawabi, Shugaba Xi Jinping ya ce, tun bayan taro karo na 19, na wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, an yi kokarin gudanar da gyare-gyare a fannoni daban daban na kasar, inda aka samu ci gaba sosai. Ya kara da cewa, a nan gaba, za a kara mai da hankali kan wasu matsalolin da ake fuskanta, tare da kara kokarin zurfafa gyare-gyare a kasar. (Bello Wang)