in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 33 sun mutu lokacin da wasu kwale-kwale suka kife a kudancin Thailand
2018-07-06 19:27:09 cri

Rahotanni daga Thailanda na cewa, har zuwa karfe 1 da mituna 40 na ranar yau agogon wurin mutane 33 ne aka tabbatar sun mutu kana wasu 23 kuma sun bace, lokacin da wasu kwale-kwale guda biyu dauke da Sinawa masu yawon bude ido suka kife a kudancin kasar.

Gwamnan lardin Phuket, Norraphat Plodthong ya shaidawa taron manema labarai a Jumma'ar nan cewa, rashin kyan yanayi ne ya haddasa hadarin biyo bayan kadawar iska mai karfi da ba a taba ganin irinta ba cikin shekaru 10 da suka gabata. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China