Dlamini, ta bayyanar harin da cewar mummunan laifi ne da 'yan tawayen na Sudan ta kudu suka kaddamar a Jakawa dake yankin Gambella na kasar Habasha a ranar 15 ga watan Aprilun 2016, wanda yayi sanadiyyar hallaka mutane 208 da kuma yin garkuwa da wasu 102 wadanda mata ne da kananan yara.
AU ta aike da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa dasu, da fatan samun sauki ga wadan suka jikkata.
Sannan ta bada tabbacin goyon bayan AU ga gwamnatin Habasha da alummar kasar.
Dlamini-Zuma ta bukaci da'a gaggauta sako mata da kananan yaran da aka yi garkuwa dasu ba tare da gindaya wasu sharruda ba.