in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da Kim Jong Un a Beijing
2018-06-20 18:48:33 cri

Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin koli na JKS Xi Jinping, ya gana da shugaban Koriya ta arewa Kim Jong Un a yau Laraba, a fadar karbar baki ta Diaoyutai dake nan birnin Beijing.

Yayin zantawar ta su, shugaba Xi ya bayyana cewa, "Suna farin ciki da ganin yadda sannu a hankali, ake aiwatar da muhimmiyar matsaya da Sin tare da Koriya ta arewa suka cimma. Da kuma irin alakar abota da hadin gwiwa dake wanzuwa tsakanin sassan biyu, dama irin yadda hakan ke haifar da sabon karsashi, da damar ci gaba da tattaunawa, wadda za ta sassauta halin da ake ciki a zirin Koriya.

Shugaban na Sin ya ce, ana karfafa wannan mataki, kana hanyar da jam'iyyar WPK mai mulki a Koriya ta arewa ke dauka a yanzu, ta dore salon mulkin gurzuwa kan wata sabuwar sahihiyar turba.

Ya ce, ya yi imanin hadin gwiwar kasashen biyu, zai samar da alfanu gare su, da ma jama'ar su baki daya. Kaza lika Sin a shirye take ta yi musayar kwarewa da Koriya ta arewa, kana su hada karfi, da hadin kai, domin samarwa salon mulkin gurguzu sahihin ginshiki a kasashen biyu domin gaba.

A nasa bangare kuwa, shugaba Kim Jong Un cewa ya yi, ziyararsa yanzu haka a Sin, ta samar wa bangarorin biyu wata kyakkyawar dama, ta zurfafa kawance tsakanin sa da shugaba Xi, tare da zurfafa alakar dake tsakanin sassan biyu.

Daga nan sai ya jaddada alkawarin ci gaba da aiki tare da bangaren na Sin, wajen daga martabar alakar sassan zuwa wani sabon matsayi, tare da taka rawar gani wajen ba da kariya ga sassan duniya, da kuma daidaito a yankin da suke.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China