in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta kudu ta karyata wasu rahotanni game da rashin lafiyar shugaban kasar
2018-05-03 10:13:37 cri

Mai magana da yawun fadar shugaban kasar Sudan ta kudu Ateny Wek Ateny ya karyata wasu rahotannin da tsohon likitan kasar ke cewa, wai shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudun ba shi da lafiya.

Ateny Wek Ateny wanda ya bayyana hakan yayin zantawa ta wayar tarho da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya bayyana rahoton a matsayin karya tsagwaronta, kuma wata farfaganda ce ta neman zubar da kimar shugaban a idon duniya.

Jami'in ya ce, shugaba Kiir yana cikin koshin lafiya, kuma yana aikinsa kamar yadda ya saba, don haka babu wani dalilin da wasu makaryata za su ce ba shi da lafiya, har ma ba zai iya jagorantar kasar ba.

A makon da ya gabata ne dai, wani tsohon likitan gwamnatin kasar, kuma tsohon ma'aikacin asibitin koyarwa dake Juba Mawien Akot, ya ce shugaba Kiir ba shi koshin lafiyar da zai jagoranci kasar.

Sai dai kuma shugaban sashin kula da lafiya na fadar shugaban kasar Sudan ta kudu Andrew Akon Akech ya karyata wannan zargi, yana mai cewa, Akot bai taba aiki a ofishin shugaban kasa da har zai iya ba da wannan shaida ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China