in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron koli na kafofin yada labarai na Asiya a  Sanya na Hainan
2018-04-09 14:19:26 cri

Yau Litini 9 ga watan nan ne a birni Sanya dake lardin Hainan, yayin da ake gudanar a dandalin Bo'ao, aka kaddamar da taron kolin kafofin yada labarai na kasashen Asiya, wanda ke da jigon "Sabon zamani na hadin gwiwa ta fuskar yada labarai-yin mu'ammala da hadin gwiwa da kirkire-kirkire."

Mamban hukumar siyasa a kwamitin tsakiya na JKS, kuma ministan hukumar kula da watsa labarai na kwamitin tsakiyar JKS Mista Huang Kunming ya halarci bikin bude taron, tare da bada wani jawabi mai jigon "Yada tunanin bude kofa da kirkire-kirkire don samun bunkasuwar Asiya gaba daya."

A cikin jawabinsa, Mista Huang ya bayyana cewa, wannan shekara, ita ce ta cika shekaru 40 da fara aiwatar da tsarin bude kofa ga kasashen waje, da yin kwaskwarima. A cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, bunkasuwar Sin na da alaka sosai da bunkasuwar Asiya, kuma ita ma ta haifar da amfani matuka ga bunkasuwar Asiya, har ma ga duk fadin duniya baki daya.

Har wa yau Sin tana fatan hada kai da kasashen Asiya, da ma na duniya baki daya, don bullo wata sabuwar hanya ta kirkire-kirkire, da rarraba ci gaban da za a samu. A halin yanzu da ake ciki na samun bunkasuwa da kwaskwarima a duniya, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da jerin tunaninsa, da ka'idarsa mai muhimmanci, ta bunkasa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, matakin da ya kasance tunani da tsari mai kunshe da hikima daga kasar Sin. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China