A cikin wasikar, Xi ya nuna cewa, taron na da ma'ana kwarai wajen inganta cudanya da hadin kai tsakanin kasar Sin da kasashen dake amfani da harshen Portugal a fannin dokokin shari'a, wanda zai samar da muhalli mai kyau ga bangarorin biyu wajen samun ci gaba tare.
Baya ga haka, Xi ya bayyana fatan wakilai mahalartan taron za su yi cudanya tare da tattaunawa sosai, don inganta gudanar da harkokin kasa da kasa da martaba da doka da oda ta hanyar yanar gizo. (Bilkisu)