in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana: An gargadi Amurka ta guji daukar matakai na kashin kanta
2018-03-25 13:16:25 cri
Kwanakin baya shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sa hannu kan wata yarjejeniyar takaitawa kasar Sin fitar da kayayyakinta zuwa kasar Amurka. Dangane da wannan batun, wasu kwararru da masana na kasar Sin, wadanda suka halarci taron tattauna batun tattalin arziki da ya gudana a gefen taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar manyan kusoshi na neman samun ci gaban kasar Sin, sun ce matakin da kasar Amurka ta dauka ya sabawa ka'idojin ciniki na kasa da kasa, wanda zai haifar da illoli ga kasar ta Sin, da Amurkar, gami da daukacin duniya baki daya. A don haka, kwararrun sun shawarci kasar Amurka da ta dakatar da matakin nan take, tare da nuna sanin ya kamata.

Wang Yiming, shi ne mataimakin darekta na cibiyar nazarin fasahohin raya kasa karkashin majalisar gudanarwar kasar Sin, wanda ya ce, matakin da kasar Amurka ta dauka na fara yin bincike kan yanayin cinikayya na kamfanonin kasar Sin, an samar da shi ne bisa dokokin cikin gidan kasar Amurka. Sai dai la'akari da cinikayyar kasa da kasa ta dokokin cikin gidan wata kasa, wani matakin ne da ya sabawa ka'idojin kasa da kasa.

A nasa bangaren, Zhu Min, tsohon mataimakin babban darektan asusun bada lamuni na duniya IMF, kuma shugaban cibiyar nazarin harkar hada-hadar kudi ta jami'ar Tsinghua ta kasar Sin, ya ce, da ma kasar Amurka daya ce daga cikin kasashen da suka kafa tsarin ciniki tsakanin kasashe daban daban, amma a yanzu ta riga ta zama mai barnata tsarin. A cewarsa, ko shakka batu, matakin da kasar Amurka ta dauka zai yi illa ga moriyar kasar Sin, yayin da a wani bangare na daban, zai yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin Amurkar, da tsarin ciniki na kasa da kasa.

Zhu ya kara da cewa, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta riga ta sanar da jerin wasu kayayyakin kirar kasar Amurka da aka shigo da su kasar Sin, wadanda za a kara karbar harajin kwastam a kansu. A cewar Zhu, wannan wata alama ce da kasar Sin ta nuna, cewa kasar ba za ta ji tsoron matakin da kasar Amurka ta dauka ba. Sa'an nan kasar Sin ta sha yin gargadi ga kasar Amurka har karo da dama, inda ta bukaci kasar Amurkar da ta nuna sanin ya kamata, don gudun kada "ta yi tuya ta manta da albasa".(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China