in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sanya kudin hajarin kayayyaki mafi yawa a cikin shekaru 20 a Afrika ta kudu
2018-02-22 12:39:37 cri
Ministan kudin kasar Afrika ta kudu Malusi Gigaba, ya sanar da karin kudaden harajin kayayyaki wato VAT a lokacin jawabinsa na farko na kasafin kudin shekarar 2018/19 wanda ya gabatar a ranar Laraba. Wannan kari shine irinsa na farko da aka samu a kasar sama da shekaru 20 da suka gabata.

Ministan ya sanar da karin harajin na VAT da kashi 1 bisa 100 wato daga kashi 14 zuwa kashi 15 bisa 100. Manufar kara kudaden na VAT da sauran kudade haraji da kasar ta kuduri aniyar aiwatarwa shi ne, domin samun karin kudaden shiga da yawansu ya kai kudin kasar Rand biliyan 36, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 3.09, inji ministan.

Kasar Afrika ta kudu tana fuskantar gibin kudaden shiga da yawansu ya kai Rand biliyan 48.2 kwatankwacin dala biliyan 4.1, inda masana tattalin arziki suka yi hasashen cewa ministan bashi da wani zabi illa ya kara kudaden na VAT.

Wani masanin tattalin arziki na Standard Bank Elna Moolman, yayi gargadi tun gabanin tsara kasafin kudin kasar. Moolman ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, karin kudaden harajin na VAT wani kyakkyawan tunani ne sai dai talakawa ba za su laminci karin ba a yayin da ake jajiberen manyan zabukan kasar a shekarar 2019.

Gigaba ya ce, ba'a yi sauye sauye kan tsarin na VAT ba tun a shekarar 1993, kuma hakan koma baya ne idan aka kwatanta da takwarorin kasar. Don haka ya ce suna ganin basu da wani zabi da ya wuce su kara kudaden harajin na VAT muddin suna son ingantuwar fannin kudaden kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China